• Home  
  • Gwamna Borno Umara Zulum Ya Kashe N100bn A Kan Harkar Tsaro A 2025.
- Babban Labari - Labarai

Gwamna Borno Umara Zulum Ya Kashe N100bn A Kan Harkar Tsaro A 2025.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama. Zulum ya yaba wa jami’an tsaro […]

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa ta kashe kusan Naira biliyan 100 a wannan shekara domin inganta tsaro a faɗin jihar.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Sarkin Uba, inda ya yi masa jaje kan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Zulum ya yaba wa jami’an tsaro da al’umma kan ceto manoman mata 12 da aka yi garkuwa da su.

Gwamnan, ya ce matsalar tsaro na hana samar da manyan ayyukan ci gaba a yankin.

Ya kuma sake alƙawarin gina makarantu, asibiti, hanyoyi, cibiyar kwamfuta, cibiyar JAMB da kuma Kwaleji a Uba.

“Ziyarar na zo ne don duba yanayin tsaro. Zan gana da jami’an tsaro domin tabbatar da Askira/Uba sun samu kariya.

“Ba za a samu zaman lafiya ba idan babu tsaro. Muna da shirin samar da hanyoyi, ilimi da kiwon lafiya,” in ji Zulum.

Sarkin ya gode wa gwamnan; “Ka yi mana abubuwa da dama. Da doka za ta ba da dama, da mun roƙe ka, ka ci gaba da mulki. Allah Ya yi maka albarka.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai