Rundunar yan sandan jihar Kano ta fara shirin ganin tabbatar da babban zaɓen shekarar 2027, inda ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki domin gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan zaɓen 2027 da aka gudanar a Mambayya House, Kano.
CP Bakori, ya ce rundunar ta fara horas da jami’anta kan tsaron zaɓe, dokokin aiki da kuma kare haƙƙin ɗan Adam.
Ya ce za a ƙarfafa haɗin gwiwa da INEC, jam’iyyun siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini, ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai domin dakile tashin hankali.
Haka zalika ya bayyana cewa rundunar za ta yi amfani da bayanan sirri wajen yaƙi da ’yan daba, yaɗuwar makamai, shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaɓen.
Ya kuma yi gargaɗin cewa ba za su lamunci satar akwatin zaɓe ko tashin hankali ba, inda ya ce za a samar da jami’an kai daukin gaggawa a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
CP Bakori ya buƙaci yan siyasa su ja kunnen magoya bayansu, yayin da ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai su guji yaɗa labaran ƙarya da kalaman da za su iya tayar da zaune tsaye.
Ya kuma shawarci matasa da su guji shiga harkar daba, yana cewa, “makomarsu na cikin haɗari.”
Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa rundunar ’yan sanda, tare da sauran hukumomin tsaro, za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya kafin zaben da lokacin yinsa da kuma bayan zaɓen 2027.
Ya buƙaci jama’a su kai rahoton duk wani abu da ba a amince ga rundunar ta lambobin 08032419754, 08123821575 da 09029292926.
