• Home  
  • Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki – Tinubu
- Siyasa

Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce zai farfaɗo tare da tabbatar da cewa matatun man ƙasar, da suka jima ba sa aiki, za su koma aiki. Shugaban Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Alhamis, lokacin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) suka kai masa ziyara a fadarsa. […]

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce zai farfaɗo tare da tabbatar da cewa matatun man ƙasar, da suka jima ba sa aiki, za su koma aiki.

Shugaban Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Alhamis, lokacin da Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG) suka kai masa ziyara a fadarsa.

Da yake mayar da martani kan matsalolin ƙungiyar ta bayyana, Tinubu ya ce matatun ba sa aiki yadda ya kamata a yanzu.

Ya jaddada cewa dole ne matatun su kasance masu riba tare da samar da amfanin da aka gina su domin sa.

Tinubu ya kuma ce ya ɗauki alhakin gyara kadarorin da kuma matsalolin da gwamnatocin da suka gabata suka bari, ba tare da la’akari da abin da ya faru a baya ba.

“Ni ba mutum ba ne da zan je in duba wani abu sannan in dawo in ce komai yana tafiya daidai, saboda kawai na ɓoye abubuwan da shugabannin baya suka yi.”

Ya ƙara da cewa ”ko ma mene ne ya faru a shekarun baya, yanzu alhakina ne a matsayina na shugaban ƙasa in gyara abubuwan, in tabbatar suna aiki yadda ya kamata domin amfanin mafi yawan al’ummar ƙasar nan”.

Shugaban na Najeriya ya ce ya ɗauki wannan alhakin, kuma zai aiwatar da shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai