Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci taron majalisar zartarwa na jihar a jiya Litinin, Inda a yayin taron aka rantsar da sabbin kwamishinoni guda 3
Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗar da:
1- Hajiya Amina S. Abdullahi (HOD) a matsayin kwamisiniyar ma’aikatar ayyuka na musamman.
2. Hon. Ibrahim Namadi Dala Kwamishinan Ma’aikatar Duba Ayyuka da Nagartar Aiki.
3. Prof. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin kwamishinan ma’aikatar kuɗi.
Yayin bikin rantsuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya sabbin kwamishinonin murna tare da horar su da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana.