Gwamnan kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya ayyana kadarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa’ar ma’aikata.
Sanarwar da ofishin gwamnan mai jiran gado ya fitar a jiya juma’a ta ce abba kabir yusuf ya gabatar da kansa ga ofishin hukumar ɗa’ar ma’aikata da ke Kano tare da miƙa fom da ya cike na ƙadarorinsa.
Ya ce “Na cika sharuɗɗan da kundin tsarin mulki ya gindaya na ayyana ƙadarorin da na mallaka kafin rantsar da ni a 29 ga mayu,” in ji Abba.
Gwamnan mai jiran gado ya kuma bayyana cewa dukkanin jami’an da za su yi aiki a gwamnatinsa da suka ƙunshi har da muƙaman siyasa sai sun bayyana ƙadarorinsu kamar yadda doka ta tanada.
A ranar litinin 29 ga mayu ne za a rantsar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin sabon gwamnan jihar Kano.