Home » Nasarawa: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kame Masu garkuwa da Mutane 26

Nasarawa: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Kame Masu garkuwa da Mutane 26

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Nasarawa: Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Kame Masu garkuwa da Mutane 26

Rundunar ‘yan sandan najeriya reshen jihar nasarawa ta sanar da nasarar kama wasu mutane 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke addabar mazauna jihar.

Rundunar ta kuma ce jami’anta sun ceto biyu daga cikin mutane da aka yi garkuwa da su kwanan nan daga karamar hukumar wamba da ke jihar a samamen da suka kai.

Da yake gabatar da dukkan wadanda ake zargi da aikata laifuka da aka kama da laifuka daban-daban a fadin jihar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, dsp ramhan nansel, ya ce rundunar ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da suka addabi mazauna karamar hukumar karu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?