Home » Gwamnan Kano Ya Kori Kwamishina da Mai Ba Shi Shawara

Gwamnan Kano Ya Kori Kwamishina da Mai Ba Shi Shawara

by Anas Dansalma
0 comment
Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya kori Kwamishinan Kasa da Tsare-tsare, Adamu Kibiya, da kuma mai ba shi shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni, Aliyu Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye.

Tsohon kwamishinan Kasa da Tsare-tsare, Adamu Kibiya

An kore su ne bisa munanan kalamai da suka furta a jiya a wajen addu’a ta musamman da aka gudanar.

Aliyu Imam(Ogan Ɓoye)

Wannan na zuwa ne bayan sakin wani bidiyo wanda a ciki aka ga kwamishina Adamu Aliyu Kibiya  a yayin taron addu’a na musamman da aka yi, inda magoya bayan jam’iyyar ta NNPP suka yi barazana ga masu shari’a kan shari’ar da ake tsakanin jam’iyyun APC da NNPP.

Wannan ce ta sa Kungiyar Lauyoyi ta ƙasa ta buƙaci gwamnan Kano da ya ɗauki mataki kan kwamishinan a matsayin wata hanya ta nisanta gwamnatinsa da waɗancan munanan kalamai.

Hakan ne ya sanya kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya fitar da sanarwa da ta tabbatar da korar kwamishinan da kuma mashawarci ga gwamnan.

Sannan ya tabbatar da cewa waɗancan kalamai da aka yi kan masu shari’ar da kuma mataimakin shugaban ƙasar, babu hannun gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin ba su da hurumin yin hakan.

Daga nan gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa, daga yanzu ba a yarda wani jami’in gwamnati ya yi magana ba, idan ba ta shafi ofishinsa ba, har sai ya samu izinin yin hakan.

Sannan gwamnan Kano ya umarce ma’aikatar yaɗa labarai da ta tabbatar da cewa kafafen yaɗa labarai a jihar nan, musammman na rediyo na bin ƙa’idojin da aka tanada na gudanar da ayyukansu.

A ƙarshe, gwamnatin Kano ta buƙaci al’ummar jihar nan da su kasance masu bin doka a yayin da ake jiran hukuncin da gwamnati za ta yanke game da ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar da take ƙalubalantar nasarar da NNPP ta samu a zaɓen da aka yi a Kano.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi