Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu halartar jana’izar Alhaji Sani Abdussalam Gwarzo, yaya ga mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
A cewar gwamnan, wannan babban rashi ne a daidai lokacin da jihar ke buƙatar shawarwari daga gare shi a matsayin wanda ya ga jiya, ya ga yau.
Inda gwamnan ya yi masa addu’ar Allah ya jiƙansa da rahma tare da saka masa da gidan Aljanna Firdaus.