Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su riƙa shirya tarukan tsaro domin ƙarfafa tsaro tsakanin garuruwan jihar.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwmanan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamnan Abba Kabir ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayarsu a tsakanin al’umman garuruwa da jami’an tsaro.
Matakin na zuwa ne yayin da ake sa ƙara samun rahotonnin hare-haren ƴanbindiga a ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da jihar Katsina, mai fama da matsalar tsaro.
Gwamnan ya ayyana ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa da Tudun Wada da Doguwa da kuma Gwarzo a matsayin ƙananan hukumomin da ke buƙatar kulawar tsaro ta musamman, saboda barazanar tsaro da ake sa mu a yankunan.

