Tsohon Shugaban karamar hukumar Ungoggo, Sule Musa Kadawa ya fice daga PDP zuwa APC a jihar Kano.
Rahotanni na cewa, Kadawan ya samu goyon bayan wasu yayan Jam’iyar NNPP kusan 2,000 da suka marasa baya wajen koma APC gidan A. A. Zaura.
A Yan kwananan dai an samu sauyin sheka daga jam’iyun Adawa zuwa mai mulki, inda yan Adawa da gwamnati mai ci suka zarge ta da yunkurin mayar da Jam’iya daya zargin data Musanta.
Sule Kadawa, ya bayyana cewa ya fice daga PDP ne Saboda halaye nagari da A. A. Zaura yake da su da kuma taimakon da yake yi ga marasa karfi.
Ko a Yan kwanakinnan an samu ficewar wasu Yan majalisa tarayya daga mabambantan jami’iya inda suka koma APC.

