Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi naɗe-naɗen farko na waɗanda za su taimaka masa wajen tafiyar da gwamnati.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Nakwada ne ya sanar da haka a wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Hakokin Kafafan sadarwa na zamani ga Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu kuma ya raba wa manema labarai a Gusau babban burnin jihar.
Sulaiman ya ce, gwamnan ya naɗa Alhaji Abubakar Nakwada a matsayin sakataren gwamnatin jihar. Haka kuma ya naɗa Mukhtar Lugga a matsayin Shugaban Ma’aikata.
Gwamnan Jihar, ya kuma amince da naɗin Sharifudden F. Jatto a matsayin Babban Sakataren Gwamna; sai Imran Rufa’i Ahmad, a matsayin Mataimaki na Musamman ga Gwamna.
Yayinda Ali Akilu Bungudu ya zama babban mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziki.