Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara zagaye na ƙarshe aa shirinta na kwaso ’yan ƙasar da suka maƙale a Afirka ta Kudu, tana mai gargaɗin cewa har yanzu lamarin tsaro na cike da rashin tabbas, kuma babu alamar cewa hare-haren ƙin baƙi suna raguwa.
Gwamnatin ta buƙaci ’yan Najeriya da ke ganin rayuwarsu na cikin haɗari su yi amfani da damar da ta rage ta jiragen kwaso, tana mai jaddada cewa ba za ta iya ba da tabbacin tsaron waɗanda suka zaɓi ci gaba da zama a ƙasar ba a halin da ake ciki.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta wallafa a shafinta na X.
Ministar ta buƙaci ’yan Najeriya da har yanzu ba su yanke shawarar komawa gida ba su yi nazari sosai kan haɗarin da ke gabansu, tana mai cewa dukiya da jari za a iya maye gurbinsu, amma ba za a iya maye gurbin rai ba.
Sabon gargaɗin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da kisan ’yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu, wato Emeka Charles Iroegbu, wanda rahotanni suka ce jami’an ’yan sandan Tshwane da ke Pretoria sun kashe, da kuma Musa Yunana Joe, wanda aka fi sani da Big Joe, wanda aka harbe a gaban shagonsa a Witbank da ke lardin Mpumalanga.
Gwamnatin ta kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata kisan a gaban kotu.
A cikin sanarwar, Odumegwu-Ojukwu ta ce gwamnatin Najeriya na matuƙar damuwa da lafiyar ’yan ƙasarta a Afirka ta Kudu yayin da hare-haren ƙin baƙi ke ci gaba.
“Najeriya ta damu ƙwarai da gaske game da tsaron ’yan ƙasarta a Afirka ta Kudu sakamakon zanga-zanga da hare-haren ƙyamar baƙi, musamman bayan mutuwar Musa Yunana Joe da Charles Iroegbu a cikin waɗannan hare-hare,” in ji ta.
Ta bayyana cewa gwamnati ta tsawaita wa’adin kammala aikin kwaso mutanen, wanda tun farko aka tsara zai ƙare a ranar 30 ga Yuni, saboda ci gaba da tabarbarewar yanayin tsaro.
“Babu wata alama da ke nuna cewa lamarin na ingantuwa,” in ji ministar.
Ta sake yin kira ga ’yan Najeriya da ba su yanke shawarar komawa gida ba da su yi la’akari da haɗarin da ke tattare da ci gaba da zama.
Da yake ƙarin bayani kan shirin kwaso mutanen, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya ce wani jirgin kamfanin Air Peace zai tashi daga Legas zuwa Johannesburg da misalin ƙarfe 3:30 na rana a ranar Talata domin ci gaba da aikin kwaso ’yan Najeriya da suka amince su dawo gida.
