• Home  
  • Gwamnati Ta Fitar Da Sunan Mutum 48 Da Ake Zargi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya
- Babban Labari

Gwamnati Ta Fitar Da Sunan Mutum 48 Da Ake Zargi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya

Gwamnatin Tarayya, ta fitar da sunan mutane da ƙungiyoyi 48 waɗanda ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya. Hukumar da ke sanya takunkumi ta Najeriya (Nigeria Sanctions Committee) ce, ta bayyana jerin sunayen a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026. Sunayen ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da bincike ya nuna […]

Gwamnatin Tarayya, ta fitar da sunan mutane da ƙungiyoyi 48 waɗanda ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.

Hukumar da ke sanya takunkumi ta Najeriya (Nigeria Sanctions Committee) ce, ta bayyana jerin sunayen a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026.

Sunayen ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da bincike ya nuna suna da alaƙa da ayyukan tada ƙayar baya.

Daga cikin waɗanda aka ga sunansu har da mambobin ƙungiyoyi irin su IPOB, Ansaru, da kuma ƙungiyar ISWAP.

Wasu daga cikin fitattun mutane da sunansu ya bayyana cikin jerin, sun haɗa da Simon Ekpa da Tukur Mamu.

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa wannan matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarinta na gano tare da toshe hanyoyin da ake bi wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Hakazalika, Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe asusun bankunan waɗanda cikin jerin sunayen da aka fitar.

Ga sunayensu cikin hotuna a ƙasa:

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai