Gwamnatin Tarayya ta maka Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a kotu, kan zargin kutsen intanet a layin sadarwar Mashawarcin Shugaban Kasa kan sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Hukumar Tsaro ta DSS ce ta shigar da kara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda take tuhumar El-Rufai da laifuka uku masu alaka da kutsen intanet.
A cewar DSS, karar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 ta kunshi tuhuma uku da suka shafi karya dokar Manyan Laifuka na Intanet da kuma Dokar Sadarwa ta Najeriya.
Takardar tuhume-tuhumen da DSS ta gabatar ta ce, “A ranar 13 ga Fabrairu, 2026, yayin da yake tattaunawa a shirin Prime Time na Arise TV a Abuja, El-Rufai ya amsa cewa shi da wasu abokansa sun kutsa cikin sadarwar waya ta NSA, Nuhu Ribadu. Wannan ya saba wa dokar laifukan intanet na 2024.
- Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC
- Babandede Ya Sabunta Rajistarsa A APC, Ya Samu Gagarumar Tarba.
“A wannan hira, El-Rufai ya bayyana cewa yana da alaka da wasu da suka kutsa cikin sadarwar Ribadu, amma bai kai rahoto ga hukumomin tsaro ba. Wannan ya saba wa sashen 27(b) na dokar.
Haka kuma, DSS ta ce shi da wasu da ba a kama ba sun yi amfani da na’urori da suka kutsa cikin sadarwar Ribadu, abin da ya kawo barazana ga tsaron ƙasa da kwanciyar hankali. Wannan ya saɓa wa Hukumar Sadarwa ta Ƙasa.

