• Home  
  • Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC
- Babban Labari - Labarai

Kashim Shettima ya isa Kano domin karɓar gwamna Abba zuwa APC

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa jihar Kano domin karɓar gwamnan Abba zuwa jam’iyyar APC, a wani muhimmin taron siyasa da ya ja hankalin jama’a. An shirya taron karɓar gwamnan ne a hukumance a filin wasan Sani Abacha Stadium, inda dubban magoya baya da shugabannin jam’iyya suka fara taruwa tun da wuri. Rahotanni sun […]

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa jihar Kano domin karɓar gwamnan Abba zuwa jam’iyyar APC, a wani muhimmin taron siyasa da ya ja hankalin jama’a.

An shirya taron karɓar gwamnan ne a hukumance a filin wasan Sani Abacha Stadium, inda dubban magoya baya da shugabannin jam’iyya suka fara taruwa tun da wuri.

Rahotanni sun ce an ɗauki matakan tsaro na musamman domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin.

Shettima ya isa wurin ne tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, tare da gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, Sokoto, Imo, Yobe da Katsina, lamarin da ya nuna muhimmancin taron a fagen siyasar ƙasa.

Haka kuma shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas na cikin manyan baƙin da suka halarci taron.

Masu sharhi na ganin cewa wannan sauya sheƙa na gwamnan na iya sauya yanayin siyasar jihar da ma yankin Arewa, musamman ganin irin manyan shugabannin da suka halarta domin nuna goyon baya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai