• Home  
  • Gwamnatin Edo Ta Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Arewa
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Edo Ta Yi Allah-wadai Da Kisan ‘Yan Arewa

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da kashe wasu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata, wato 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan a matsayin na dabbanci. Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, […]

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Allah-wadai da kashe wasu matafiya ‘yan Arewacin Najeriya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata, wato 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan a matsayin na dabbanci.

Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, wanda a ciki aka nuna wasu matasa sun zagaye wasu mutane da ake tunanin mafarauta ne ƴan arewa da suka taso daga kudancin ƙasar za su koma gida wataƙila domin bikin sallah.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Fred Itua ya fitar, ya ce, “Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai