Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dalilan dake janyo rashin zartar da hukunci.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ne ya bayyana hakan yayin zantarwarsa da wakilin mu yau litinin.

Wannan dai na zuwa bayan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, lamarin da ya jefa al’ummar jihar Kano cikin alhini.

‘’ da zaka ga hukunce-hukuncen laifukan da aka yanke hukunci ana daukaka kara, kaga idan an daukaka kara babu wannan damar har sai an kammala zuwa kotun koli’’.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Abdulkarim Kabiru Maude, SAN,ya ce gwamnatin Jihar Kano zata tabbatar da an yi bincike mai inganci kuma tare da yin  shari’ar cikin kankanin lokaci.

Ya kara da cewa gwamnatin Kano, tana nuna alhininta ga iyalan wadanda wannan abu ya faru da su da sauran al’ummar jihar tare daukar matakan dakile faruwar hakan.

Kabiru Maude, SAN, ya ce ma’aikatar shari’a tana daukar matakai don a tabbatar an yi bincike mai inganci, don an yankewa wadanda ake zargin hukuncin.

Haka zalika ya kara da cewa za su yi iya bakin kokarinsu don ganin hakan ya tabbata.

Gwamnatin ta yaba wa rundunar ƴansandan jihar bisa gaggawar ɗaukar matakin binciken da ya kai ga waɗanda ake zargi da aikata laifin.

A cewar sanarwar, wannan mataki na nuna ƙudirin hukumomin tsaro na kawar da aikata laifuka da dawo da aminci a zukatan jama’a da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *