Home » Gwamnatin Kano na daura auren zaurawa a yau

Gwamnatin Kano na daura auren zaurawa a yau

by Anas Dansalma
0 comment
Gwamnatin Kano na daura auren zaurawa a yau

A yau Juma’a 13 ga watan Oktoba ne gwamnatin jihar Kano ke ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa.

Tun bayan hawansa mulki ne, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanar da cewa zai yi wa matan da suka nuna sha’awarsu ta shiga shirin auren gata ta hanyar samar musu da dukkan kayayyakin da mace ke buƙata a gidan aure da kuma yi musu walicci.

Hukumar Hisbah a jihar ƙarƙashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa ta ce ta jagoranci kammala matakai biyar cikin bakwai na auren, inda za a ɗaura aurarrakin a masallatai a dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

Kamar yadda jami’an hulda da jama’a na rundunar ta Hisbah ya bayyana wa muhasa da wannan safiya, ya ce za a ɗaura auren ne bayan sallar juma’a a Masallacin gidan sarki dake cikin gari da kuma masallacin waje dake unguwar Fagge.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi