Daga: Halima Djimrao
Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana damuwarta kan asarar Naira Miliyan dubu 10 da manoman citta suka yi, a kudancin jahar Kaduna sakamakon barkewar wata cuta mai suna Fungi Pathogens.
Manema labarai sun ce Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu Sunday Katung na jam’iyar PD, ne ya gabatar da kudirin a zauren majalissar ranar Talata, inda yace cutar ta lalata fiye da kadada dubu 2 da 500 na gonakin cittar , da kudinsu ya kai sama da Naira miliyan dubu 10 , a fadin kananan hukumomi 7 na jahar Kaduna.
Sanatan ya kara da cewa matukar ba a dauki mataki da wuri ba, lamarin zai shafi yadda Najeriya ke fitar da citta zuwa sashen duniya, kasancewar jahar Kaduna ce a sahun gaba wajen noman citta a Najeriya, da kuma fitar ita sassan duniya daban-daban.
Sanatan yace daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2018 an noma citta ton dubu ɗari uku.
Majalissar Dattawan ta bukaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da ma’aikatar noma ta kasa da kuma cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC, su dauki matakin gaggawa don dakile yaduwar cutar.