Home » Gwamnatin Kano na shirin ingata kasuwar Dawanau

Gwamnatin Kano na shirin ingata kasuwar Dawanau

by Anas Dansalma
0 comment
Hukumar bunƙasa harkar noma ta jihar Kano (KSADP), za ta kashe kimanin Naira miliyan 600 domin gudanar da ayyukan inganta kasuwar hatsi ta kasa da kasa da ke Dawanau.

Hukumar bunƙasa harkar noma ta jihar Kano (KSADP), za ta kashe kimanin Naira miliyan 600 domin gudanar da ayyukan inganta kasuwar hatsi ta kasa da kasa da ke Dawanau.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Malam Ameen Yassar, kwararre a fannin kula da ayyuka, ya fitar wanda kuma shi ne zai gudanar da ayyukan.

Yassar ya ce, Bankin ci gaban Musulunci (IsDB) tare da hadin guiwar Asusun inganta jin dadin rayuwa (lives and livelihood funds) ne suka dauki nauyin shirin.

Ayyukan da za a gudanar, sun hada da titi mai nisan kilomita hudu, da magudanar ruwa da fitulun kan titi.

Ya ƙara da cewa an bayar da wannan kwangilar ne ga kamfanin Labour Technical Services Ltd, kan kuɗi Naira miliyan 508.

Yassar ya kara da cewa, an bai wa kamfanin AITEC Infraconsult Ltd kwangilar gina gidan wanki guda uku da masallaci da ofishin ‘yan sanda da ofisoshi da dakin taro, a kan kudi naira miliyan 92.

 A ƙarshe, ya ce, ana sa ran za a kammala aikin cikin watanni 12.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?