A yayin da musulmai ke cigaba da murnar tunawa da ranar da aka haifi Annabin tsira, Annabi Muhammad (SAW).
Inda gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon taya al’ummar musulmi murnar wannan wata mai albarka.
Wannan saƙo ya fito ne ta bakin sakataren yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya ce gwamnan ya shawarci al’umma da su yi ko yi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) na haƙuri da juriya da yafiya da kuma kyautata wa abokan zama, cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
Sannan gwamnan ya ja hankalin matasa kan su yi nazarin rayuwar Annabi da Sahabbansa tare da amfani da darusan da ke cikin rayuwarsu wajen mu’amalantar junansu da ma al’umma bakiɗaya.
A ƙarshe, ya roƙi al’umma da su yi bikin maulidin cikin lumana da yin addu’o’i na neman zaman lafiya da tsaro ga jihar nan da ma ƙasa bakiɗaya. COV. AM/AS