Home » Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin tatance daliban da za ta dau nauyin karatunsu

Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin tatance daliban da za ta dau nauyin karatunsu

by Anas Dansalma
0 comment
Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin tatance daliban da za ta dau nauyin karatunsu

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala shirin daukar nauyin dalibai 1,100 da za’a tura domin karatun digiri a jami’o’in ciki da wajan ƙasar nan.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jiha, Dokta Yusuf Kofar-Mata ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a nan Kano, inda ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta kaddamar da kwamitin mutum tara domin tantance masu neman gurbin karatun.

Kwamishinan ya ce, sun karbi sakamakon dalibai 1,200, daga ciki sun tantance sama da 800 ciki har da masu digirin farko.

Dr, Yusuf Kofar Mata ya ce, “Za a dauki nauyin dalibai dubu daya da dari daya a rukunin farko. Haka kuma kamitin na ci gaba da gayyata tare da tantance wadanda suka nemi tallafin.

Ya kara da cewa, suna saran bayan kammala karatun, da yawa daga cikin daliban za su dawo da dabaru da sauran damammaki da za su tallafa wajan inganta harkokin kasuwanci, bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa baki daya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi