Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara shirin raba Naira dubu ashirin ga dalibai mata dubu arba’in da biyar a matsayin tallafi domin ƙarfafa wa iyaye su riƙa tura ‘ya’yansu makaranta.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a yayin gudanar da bikin ranar samun ‘yancin Najeriya karo na sittin da uku da aka yi a Sani Abacha Stadium.
Ya kuma ce za a dawo da motocin da ke kai yara mata zuwa makaranta tare da dawo da su unguwanninsu.
Sannan gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta gina karin makarantu a ƙananan hukumomi 44 da ke jihar nan domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ko da ke yawa a tituna.
A irin wannan yunƙuri ne, gwamnatin ta shirya aikewa da ɗalibai dubu ɗaya da ɗaya ketare domin yin digiri na biyu da suka samu sakamakon mai daraja ta ɗaya a digirinsu na farko.