• Home  
  • Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya
- Babban Labari

Gwamnatin Katsina ta haramta sana’ar POS da cajin waya

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da sana’ar cirar kuɗi ta PoS da cajin waya da kuma haya da babur a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da Musawa ta Jihar nan take. Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan […]

Gwamnatin Katsina ta haramta gudanar da sana’ar cirar kuɗi ta PoS da cajin waya da kuma haya da babur a yankin Ƙaramar Hukumar Matazu da Musawa ta Jihar nan take.

Sabuwar dokar zartarwar da Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanya hannu ta kuma haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a fadin jihar nan take, a matsayin wani mataki na daƙile ayyukan da ake zargin suna taimaka wa harkokin ’yan bindigar.

Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya sanar cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan ne baya zaman gaggawa da ta yi da shugabannin tsaro da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa rahotanni sun nuna cewa ’yan ta’adda na amfani da shagunan POS da wuraren canjin waya da kuɗi wajen gudanar da harkokinsu na kuɗaɗe da kiyaye-kirayen waya.

Kazalika ya bayyana cewa haramcin da aka sanya kan sayarwa ko ɗaukar man fetur a jarkoki a jihar na da nufin daƙile yiwuwar isar man fetur ga ’yan ta’adda a maɓoyarsu da ke cikin dazuka.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya ce rahotannin sirri sun nuna cewa safarar mai a cikin cikin mazubai na taimakawa ci gaba da ayyukan ta’addanci, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki mataki mai tsauri domin katse hanyoyin samar da kayan buƙatun ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Haka kuma, umarnin rufe dukkan cibiyoyin hada-hadar POS da wuraren cajin wayoyi na kasuwanci a Kananan Hukumomin Matazu da Musawa nan take na da alaƙa da rahoton binciken jami’an tsaro da ya nuna cewa ana amfani da wasu daga cikin cibiyoyin wajen saukaka sadarwa da hada-hadar kudi ga masu aikata laifuka.

“Mahukunta sun yi imanin cewa wannan zai rage wa ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane damar zirga-zirga, kasancewar galibi suna amfani da babura wajen kai-komo tsakanin al’ummomi,” in ji sanarwar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000