• Home  
  • Gwamnatin Kebbi ta ƙaryata rahoton mutuwar yara saboda yunwa
- Babban Labari

Gwamnatin Kebbi ta ƙaryata rahoton mutuwar yara saboda yunwa

Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce babu gaskiya a rahoton ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, MSF, kan mutuwar ƙananan yara sakamkon cutar tamowa a jihar. Wani rahoto da MSF ta fitar ya nuna damuwa kan ƙaruwar alƙaluman UNICEF da ke nuna cewa ana rasa kusan yara 30 cikin 100 […]

Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce babu gaskiya a rahoton ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, MSF, kan mutuwar ƙananan yara sakamkon cutar tamowa a jihar.

Wani rahoto da MSF ta fitar ya nuna damuwa kan ƙaruwar alƙaluman UNICEF da ke nuna cewa ana rasa kusan yara 30 cikin 100 ƴan ƙasa da shekara biyar a kowace rana sakamakon rashin abinci mai gina jiki, kuma kusan rabin mace-macen na faruwa ne a jihar Kebbi.

Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na jihar Yakubu Ahmed, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ba ta gamsu da ƙididdigar da aka fitar ba.

Gwamnatin ta kuma buƙaci MSF da UNICEF su gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da rahoton saboda sun san abin da aka faɗa bai faru ba.

“Gaskiya muna taƙaddama da wannan ƙididdiga da suka bayar”. Idan hakan na faruwa, mu a matayin gwamnati ya kamata mu fara sani.”

“A ce yara suna mutuwa cikin ɗarurwa a kowace rana a jihar Kebbi ba tare da gwamnati ta sani ba, abin mamaki ne.Shi ya sa muke son su kawo mana shaida, dan mun san ba ta faru ba, babu wannan mutuwa da suka faɗa,” in ji shi.

Gwamnati ta kuma buƙaci su nemi afuwa kan kuskuren da suka yi, idan suka kaa gabatar da hujja.

“Ko su ba mu hujja, ko su ba da haƙurin cewa hakan bai faru ba.” in ji kwamishinan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000