Gwamnatin tarayyar ta amince ta dakatar da yankar kudade daga asusun jihohi a kan bashin London da Paris Club.
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa takwarorinsa bayani a ganawar da suka yi jiya Talata a Abuja.
Haka kuma ya ce ministar kudi ta yi alkawarin tabbatar da ganin an mayarwa da jihohin kudin da aka yanke a baya.
A baya-bayan nan batun yankar kudin na Paris Club ya kasance babban abin takaddama tsakanin gwamnatin tarayyar da gwamnatin jihohi.
Takardar bayan taron ta kuma nuna cewa an samu sabon shugabanci a kungiyar inda mambobin suka amince ta hanyar sasantawa.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ne ya zama sabon shugaba, yayin da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya zama mataimaki.