Gwamnatin jihar Sakkwato ta ƙaddamar da motocin tasi na alfarma ga mata zalla.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin ta amince da kashe naira biliyan ashirin da dubu ɗari uku domin a siyan motoci na sufuri ga mata zalla da kuma siyan kayan abinci da za a raba musu.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗau wannan mataki ne domin rage wa mata a jihar raɗaɗin cire tallafin man fetur.