Gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari ta sake kafa sabon tarihi a harkar sufurin jiragen sama, inda ya kafa jami’an tsaron filin sauka da tashin jiragen sama masu ɗauke da bindigogi (AVSEC) a ranar juma’a.
Ministan sufurin jiragen sama sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa ba’a taba samun cigaba kamar haka haba wajen inganta harkokin tsaron kasa, ya kara da cewa yana da tabbacin cewa dukkan daliban sun sami horo mai inganci da kuma kyawawan halaye da dabi’u.
Da yake bai wa sabbabin jami’an tsaron da suka yaye masu dauke da bindigu da sauran kayan kare kai shawarwari, ya bayyana cewa ya kamata su yi aiki bisa ka’idodin horon da suka samu.
Ministan ya kara da cewa ya kan tuna da lamarin da ya faru a shekarar 2016 da jami’an Turkish airline, inda wasu fusatattun fasinjoji da suka ci karfin jami’an AVSEC a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Sirika ya kuma ba da misali da wani abu da ya faru a filin jirgin saman a jihar Sokoto inda wasu magoya bayan siyasa suka shiga kan kwaltan filin jirgin sama dake jihar Sokoto da karfin tsiya, yana mai jaddada cewa wadannan ayyuka na tabarbarewar tsaro ne da jami’an AVSEC za su iya magancewa in har suna dauke da makamai.
Ya kuma tabbatar wa da ma’aikatan cewa an samar musu da kayan yaki da sauran abubuwan more rayuwa da za su basu damar sauke nauyin da ta rataya a wuyansu na tabbatar da tsaron jami’an sufurin jiragen sama, fasinjoji dama sauran masu amfani da filin jirgin.
Ya kuma gargadi jami’an da cewa ba an samar da makaman ba ne don muzgunawa ko tsoratar da masu amfani da filin jiragen ba ne, an samar da sune domin ba wa mutanen kariya.