Rundunar sojin Najeriya ta aike da dakarunta 197 Gambia domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya, daga cikinsu akwai manyan ofisoshi 14 da kuma sojoji 183.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki 9 da tura wasu dakarun na daban zuwa kasar Guinea Bissau.
Dakarun wadanda tun a ranar 3 ga watan Afrilu suka soma horon shirin tafiya kasar a sansanin horas da masu aikin wanzar da zaman lafiya naMartin Luther Agwai International dake Jaji, a jihar Kaduna, sun shafe tsawon makonni 4 ana musu horo.
Yayin gabatar da jawabi ga dakarun na ECOWAS a lokacin da ake bikin kammala horon, Shugaban gudanarwar Taoreed Lagbaja ya ce aike dakarun ya kara nuna kudirin Najeriya a ayyukan tsaro da wanzar da zaman lafiya da ake gudanarwa a kasashen duniya. Janar Lagbaja ya kuma bukaci dakarun su mayar da hankali wajen gudanar da aikin da ya kai su bil hakki a Gambia, tare da kaucewa duk wani abu da ka iya bata sunan rundunar sojin na Najeriya.