Gwamnatin Tarayya Ta ce yanzu ‘yan ƙasar nan za su iya karɓar katin shaidar zama ɗan ƙasa ba tare da wani ƙari kan abin da suke biya ba idan za su karɓi katin cirar kuɗi.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi na Zamani, Farfesa Isa Pantami wanda ya bayyana hakan a jiya a Abuja, inda tabbatar da tuni wannan ƙuduri ya samu sahalewar majalisar zartarwa ta ƙasa.
Ya kuma ƙara da cewa wannan ƙuduri ya fito ne daga hukumar Kula da Katin Shaidar Dan Kasa, inda ta buƙaci a ba wa bankuna damar fitar da katin haɗe da na cirar kuɗi a matsayin abu guda.
A cewar Pantami, duk da cewa babu wani wuri a cikin ƙunshin dokar da ta kafa hukumar Kula da Katin Shaidar Dan Kasa, da ta ce a fitar da katin ɗan ƙasa,
Sai dai ya ce hukumar ce ta ga dacewar haɗa kai da babban bankin ƙasa CBN domin sauƙaƙa wa al’umma da ke buƙatar samun katin shaidar ɗan ƙasar.
Panatami ya kuma ce Majaliasar zartarwar ta ƙasa ta kuma sahale a haɗe bayanan layukan waya da na katin ɗan ƙasa domin tattare bayanan mutane wuri wanda hakan zai taimaka wajen samar da cikakkun bayanai na musamman.