Gwamnatin Tarayya ta fara tantancewar ƙarshe domin biyan tsofaffin ma’aikatan da aka sallama daga aiki kusan shekaru 20 da suka gabata, bayan wasu daga cikinsu sun yi fama da rashin samun cikakkun haƙƙoƙinsu na tsawon lokaci.
Daraktan-Janar na Ofishin Sauye-sauyen Ayyukan Gwamnati (BPSR), Dasuki Arabi Ibrahim, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin da yake zantawa da manema labarai a lokacin da ake gudanar da tantancewar tare da sauraron ƙorafe-ƙorafen waɗanda abin ya shafa.
Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da gudanar da tantancewar ƙarshe domin gano ma’aikatan da aka biya ƙasa da haƙƙinsu ko kuma aka hana su wasu daga cikin haƙƙoƙinsu, tare da tabbatar da an biya su abin da ya dace.
A cewarsa, an fara shirin sallamar ma’aikatan ne tsakanin shekarar 2007 zuwa 2008, amma wasu batutuwa da suka biyo baya suka sa aka ci gaba da jan lamarin har kusan shekaru 20.
Arabi ya ce BPSR na aiki tare da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin tantance sahihancin bayanan masu neman haƙƙoƙinsu, da kuma hana biyan mutanen da ba su cancanta ba.
