A yunkurin shugaban kasa na fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.
Shugaban ya ce bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, ya amince da fara biyan karin albashi na farko inda za a biya kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba.
Karin dai zai zama na tsawon watanni shida ne masu zuwa, inda kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.