Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayar da tabbacin cewar, gwamnatin tarayya a shirye take domin sake duba albashin ma’aikatanta, a wani mataki na rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Shugaban Majalisar, ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji da kuma ƴan majalisar wakilai na jihar.
Shugaban majalisar ya ce, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta cire tallafin man fetur ne domin magance matsalar cin hanci da rashawa a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar.
Ya kuma ƙara da cewar, cire tallafin ne zai sa gwamnati ta fara yaki da rashawa gadan-gadan.
Akpabio ya kuma ce idan da ba a cire tallafin man fetur ba, Najeriya ba za ta iya tafiyar da harkokinta yadda ya kamata ba a cikin shekaru masu zuwa. Inda ya ce za a sake duba batun albashin ma’aikata ne domin tabbatar da ƴan Najeriya sun yi rayuwa yadda ya kamata.