Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta ƙasa ta ce yawan man fetur da ake amfani da shi yau da kullun wanda yake kaiwa lita miliyan 46.38, ya ragu da lita miliyan 65.
A jiya ne aka samu labarin cewar, Farashin man fetur ya tashi zuwa Naira 617 a kowace lita a gidajen mai na Kamfanin Mai na Kasa.
Bayan wannan sanarwar, kamfanin man fetur na kasa ya umarci gidajen man da ke fadin ƙasar nan da su sayar da mai tsakanin Naira 480 zuwa 570 kan kowace lita, kusan kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur.
Rahotanni sun nuna cear, nan take hauhawar farashin man fetur ɗin ta haifar da karin farashin sufuri da farashin kayayyaki da sauransu.