• Home  
  • Adadin Mutanen Da Suka Rasu A Majia Sun Ƙaru Zuwa 180.
- Babban Labari - Labarai

Adadin Mutanen Da Suka Rasu A Majia Sun Ƙaru Zuwa 180.

Tun bayan Iftila’in haɗarin Tankar mai da ya faru a ranar Talata a Majiya dake Jihar Jigawa, zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasu sun kai 180 a cewar wasu mazauna yankin. Tun a ranar 15 ga watan Oktoba ne wata babbar tankar dakon man fetur tayi haɗari akan hanyar ta ta zuwa Jihar Yobe […]

Tun bayan Iftila’in haɗarin Tankar mai da ya faru a ranar Talata a Majiya dake Jihar Jigawa, zuwa yanzu adadin mutanen da suka rasu sun kai 180 a cewar wasu mazauna yankin.

Tun a ranar 15 ga watan Oktoba ne wata babbar tankar dakon man fetur tayi haɗari akan hanyar ta ta zuwa Jihar Yobe da ga Kano.

Haɗarin ya faru ne a Majiya dake ƙaramar hukumar Taura a Jihar Jigawa.

Inda nan take aka tabbatar da rasuwar kimanin mutane 150, sai kuma ƙarin wasu da suka jikkata.

Jihar dai na ta samun tallafi, a baya bayan nan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai