Gwamnonin Arewa sun yi alhinin rasuwar matar Farfesa Jega
Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun miƙa ta’aziyyarsu ga tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza. Hajiya Hadiza ta rasu ne a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci bayan gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin […]










