Shugabancin ƙungiyar Ƙwadago na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Kwamared Joe Ajearo, tayi kira da gwamnatin tarayya da ta gaggauta soke ƙarin kuɗin fetur da tayi, inda suka bayyana cewa wannan abu ne mai matuƙar bayar da tsoro. Duba da har yanzu ba’a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 ba.
Shugaban Ƙungiyar NLC na ƙasa, Joe Ajaero ne bayyana hakan a yau laraba, ya ƙara da cewa nan gaba kaɗan shugabancin ƙungiyar zai yi taro domin ɗaukar matakan da suka dace kan ƙarin kuɗin man fetur ɗin da aka yi.
Wannan na zuwa ne bayan kamfanin Mai na Najeriya{NNPC} ya bayar da umarnin ƙara farashin litar man fetur daga Naira 855 zuwa Naira 897.