Aƙalla mutum 45 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kan titin Agaie-Bida dake Jihar Naija. Hatsarin ya haɗa da wata babbar motar dakon man fetur. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Man-woro da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Lahadi. Wani mazaunin yankin ya tabbatar da a ƙalla mutane 45 ne suka rasa rayukan su.
Alahaji Wuchiko, wanda direba ne, ya bayyana cewa shi ya raka direban motar dakon man zuwa asbitin Gwamnatin tarayya na Bida.
Wani shaidar gani da ido mai suna Yahaya Muhammad ya ce sun ɗauke aƙalla gawawwaki 45 wanda duk ba’a iya ganesu, saboda yanayin ƙunar da sukayi.
Bayan tuntubar sa da aka yi, Shugaban hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta Jihar Naija Kumar Tsukwam ya sha alwashin yin bayani daga lokacin da ya sami cikakken rahoto.
Amma darakta na ma’aikatar kula da al’amura na gaggawa Alhaji Abdullaghi Arah ya tabbatar da faruwar al’amarin.