Mutanen da suka tsira da ransu a harin Gidan Mantau na karamar hukumar Malumfashin jihar Katsina sun ce yayin da ake ci gaba da neman mutanen da suka mutu a harin, ya zuwa yanzu sun gano gawarwaki 55.
Mutanen, sun ce harin da aka kai kan masallacin garin lokacin da suke sallar Asuba ranar Talata ya tagayyara su, inda suka roki gwamnatin tarayya da ta jihar su kare su daga irin wannan harin a nan gaba.
Aminiya ta gano cewa kusan kwana hudu da kai harin, har yanzu babu cikakkun bayanai a kai saboda wahalar shiga garin wanda ’yan bindiga suka tarwatsa mutanen cikinsa, lamarin da ya sa ya yi wahalar shiga ga jami’an gwamnati da masu kai agaji.
Sai dai wakilinmu da ya yi ta maza ya je har kauyen da ma makwabtansa a ranar Alhamis, y ace mutanen yankin na cikin tsaka mai wuya.
Ya ce hatta hanyar shiga garin yanzu sahu ya dauke a kanta saboda ko jami’an tsaron da za su dakile kai hari babu a kanta.
Mazauna yankunan sun ce sai da aka shafe tsawon sa’o’i kafin jami’an gwamnatin jihar su iya shiga yankin, kuma su ma a kan babbar hanya suka tsaya suka yi wa mutane jawabi ba tare da sun shiga garin ba.
Bayanai sun nuna mutanen da ba su ga danginsu ba yanzu dazuka suke shiga su duba gawarwakinsu a can.
A cewarsu, a yanzu adadin wadanda suka mutu sun kai 55, sabanin 34 da a baya hukumomi suka tabbatar.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana damuwa kan karuwar kai hare-hare a jihar ta Katsina da ma wasu jihohin na Arewa maso Yamma.
Mazauna garin dai sun ce ko a bara an kashe musu sama da mutum 20 a makamancin irin wannan harin.
Bayan kai harin masallacin, rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun rika bi gida-gida suna kashewa tare da sace mutane.
Daga cikin mutanen da aka kashe har da wasu mutum 15, dukkansu ’yan gida daya da aka kulle su a cikin gida sannan aka banka musu wuta.

