• Home  
  • Hauhawar farashi ta faɗo da kaso 23.71 a Najeriya – NBS
- Babban Labari - Labarai

Hauhawar farashi ta faɗo da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga kashi 24.23 a watan Maris ɗin 2025 zuwa kashi 23.71 a watan Afrilun 2025. Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce hauhawar farashin da aka samu a watan Afriliu ya nuna an samu ragin kaso 0.52 na hauhawar idan aka kwatanta da watan Maris. “Wannan na […]

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga kashi 24.23 a watan Maris ɗin 2025 zuwa kashi 23.71 a watan Afrilun 2025.

Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce hauhawar farashin da aka samu a watan Afriliu ya nuna an samu ragin kaso 0.52 na hauhawar idan aka kwatanta da watan Maris.

“Wannan na nuni da cewa hauhawar farashin Ta shekara-shekara Ta ragu a watan Afrilun 2025 idan aka kwatanta da watan Afrilun 2024.”

Dangane kuma da hauhawar farashin kayan abinci a watan Afrilun 2025 ta kasance kaso 21.26 kamar yadda ke faruwa a shekara-shekara.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai