Hauhawar farashi ta ragu a watan Oktoba – NBS
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce Hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ta ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ta ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba.




