• Home  
  • An samu hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kashi 22.79 a watan Yuni
- Labarai

An samu hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kashi 22.79 a watan Yuni

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a watan Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris ɗin shekarar nan.

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a watan Yuni

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya ƙaru zuwa kashi 22.79 a watan Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris ɗin shekarar nan.

A wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta ƙasa ta fitar a yau Litinin, ta ce an samu ƙaruwar ne sakamakon canjin da aka samu a farashin kayan abinci.

Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 22.25 wanda ya zarce kashi 20.60 da aka samu a watan Yunin 2022.

A ranar Alhamis 13 ga watan Yuli, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci a matsayin martani ga hauhawar farashin abinci a ƙasar.

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci, kuma a yayin da ake ci gaba da kokawa, gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur, lamarin da ya ƙara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000