• Home  
  • Hayaƙin janareta ya yi ajalin saurayi da budurwa a Kuros Riba
- Babban Labari

Hayaƙin janareta ya yi ajalin saurayi da budurwa a Kuros Riba

Hayaƙin janareta ya yi sanadin mutuwar wata budurwa da saurayinta a Ƙaramar Hukumar Kalaba ta Kudu da ke Jihar Kuros Riba. Rahotanni sun ce masoyan sun tare a sabon gidan haya ne kwanan nan. A daren ranar Alhamis, sun kunna janareta kafin su kwanta barci. An ce budurwar mai suna Favour Uduak Smith da saurayinta […]

Hayaƙin janareta ya yi sanadin mutuwar wata budurwa da saurayinta a Ƙaramar Hukumar Kalaba ta Kudu da ke Jihar Kuros Riba.

Rahotanni sun ce masoyan sun tare a sabon gidan haya ne kwanan nan.

A daren ranar Alhamis, sun kunna janareta kafin su kwanta barci.

An ce budurwar mai suna Favour Uduak Smith da saurayinta Akpan, sun kwanta barci ba tare da sanin hayaƙin janaretan na shiga cikin ɗakin ba. D

aga bisani hayaƙin ya shaƙe su har suka rasu.

Wani mazaunin unguwar Farm Centre mai suna Akong ya ce da safe aka lura janaretan ya ci gaba da aiki, sannan aka ga hayaƙi na fitowa ta saman rufin ɗakin.

Ya ce an yi gaggawar zuwa domin ceto su, amma aka tarar da ƙofar ɗakin a kulle.

An kiran sunan budurwar tare da buga ƙofa, amma ba sa amsa ba.

Daga ƙarshe aka ɓalle ɗakin, inda aka tarar sun rasu.

Mazauna yankin sun ce tun makon da ya gabata ba a samun wutar lantarki a unguwar, lamarin da ya sa mutane da dama ke amfani da janareta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kuros Riba, Sunday Eitopha, ya t

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000