• Home  
  • Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?
- Labarai

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Kusan shekara 70 ke nan da Najeriya ta gano ɗanyen mai na kasuwanci. Amma duk da wannan tsawon lokacin da ƙasar ta kasance tana fitar da miliyoyin ganga na ɗanyen, tambayar da ake yi ita ce: me wannan arziki ya kawo wa Najeriya, kuma me ƙasar ta rasa saboda dogaro da shi? A wani rahoto da ma’aikatar […]

Kusan shekara 70 ke nan da Najeriya ta gano ɗanyen mai na kasuwanci. Amma duk da wannan tsawon lokacin da ƙasar ta kasance tana fitar da miliyoyin ganga na ɗanyen, tambayar da ake yi ita ce: me wannan arziki ya kawo wa Najeriya, kuma me ƙasar ta rasa saboda dogaro da shi?

A wani rahoto da ma’aikatar man fetur ta Najeriya ta wallafa kan tarihin ɗanyen mai a Najeriya, ta ce a shekara ta 1956, kamfanin Shell-BP ya gano ɗanyen mai na kasuwanci a Oloibiri, a jihar Bayelsa ta yanzu.

Rahoton ya ƙara da cewa shekara biyu bayan, wato a 1958, Najeriya ta fara fitar da ɗanyen mai zuwa kasuwannin duniya, wanda shi ne ya buɗe wani sabon babi a tattalin arzikin ƙasar.

A wani binciken da babban bankin Najeriya CBN ya yi, ya gano cewa kafin gano mai, noma shi ne babban tushen arzikin ƙasar, wanda ke samar da kuɗaɗen shiga na gwamnati, amma daga baya kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga fitar da mai suka zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.

Ga ƙarin bayani kan wannan labarin idan kuka latsa nan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai