• Home  
  • Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya Sulaiman Abba ya fice daga jam’iyar APC.
- Babban Labari

Tsohon Sufeton ƴan sandan Nijeriya Sulaiman Abba ya fice daga jam’iyar APC.

Tohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Suleiman Abba, ya fice daga Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa. Abba ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Asabar yayin wani gangami da aka gudanar a garin Bamaina, mahaifar wani jigo na PDP kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, inda shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta suka […]

Tohon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Suleiman Abba, ya fice daga Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa.
Abba ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Asabar yayin wani gangami da aka gudanar a garin Bamaina, mahaifar wani jigo na PDP kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, inda shugabannin jam’iyyar da magoya bayanta suka tarbe shi.
‎Tsohon shugaban ‘yan sandan ya ce ya shiga jam’iyyar PDP ne domin cika burinsa na tsayawa takarar wakilcin Mazabar Sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a Majalisar Dokoki ta Ƙasa

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000