Home » ‘Yan Sanda Ta Shirya Bincike Game da Cin Hanci Don Ƙarin Girma

‘Yan Sanda Ta Shirya Bincike Game da Cin Hanci Don Ƙarin Girma

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda a Najeriya ta ce ta kafa kwamitin bincike don bin diddigin zargin cewa ana biyan sama da naira miliyan bakwai kafin a yi wa manyan jami’an ‘yan sanda ƙarin girma.

Hukumar ta yi kira ga duk wani da ke da wata shaida kan wannan zargi, DA ya bayyana gaban ta, don gudanar da bincike.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar ta ce matakan, martani ne kan wani rahoto da wata jaridar intanet a Najeriya ta buga mai taken ‘badaƙalar cin hanci ta tashi hankula a hukumar kula da aikin ‘yan sanda’.

Rahoton ya yi zargin cewa sai an biya cin hancin $10,000, kimanin naira miliyan bakwai, domin yi wa manyan ‘yan sanda ƙarin girma a hukumar.

Ta dai yi alƙawarin ɗaukar mataki a kan duk jami’in da aka samu da hannu kan zargin karɓar cin hancin.

Kwamitin a cewar sanarwar Mista Ani, ya ƙunshi jami’an rundunar ‘yan sanda da kuma na hukumar kula da aikin ‘yan sanda.

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda dai ta ce hankalinta ya kai ga wani rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa a ranar Talata 11 ga watan Afrilun 2023.

Rahoton na da taken “Badaƙalar Cin Hanci ta Gigita Hukumar kula da Aikin ‘Yan Sanda ta Najeriya inda Jami’an ‘Yan sanda ke Zargin Biyan $10,000 Kafin su Samu Ƙarin Girma.

Sanarwar hukumar ta ci gaba da ruwaito labarin da cewa, wata ƙungiya ce mai ƙumbiya-ƙumbiya da ke bayyana kanta a matsayin jami’an ‘yan sandan da suka fusata.

Fusatattun ‘yan sandan a cikin wata sanarwa da wani Mista Chijioke Okonkwo ya rubuta a madadin sauran takwarorinsa “sun nemi fadar shugaban ƙasa ta yi bincike kan badaƙalar da ake tafkawa a rundunar ‘yan sanda”.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi