Hukumar kula da ingancin kayayyakin masana’antu ta kasa (SON) ta ce, ta tura bukatar sake inganta dokokin hukumar ga majalisar dokokin kasa domin ta samu damar zartar da hukuncin da ya kamata ga masu shigowa da kayayyaki marasa inganci.
Hukumar ta SON ta ce dokar da ake da ita yanzu, tana dakile ayyukanta don haka akwai bukatar a yi mata kwaskwarima.
Darakta Janar na hukumar, Farouk Salim ya ce sun riga sun mika wa majalisa bukatar gyaran kundin dokokin hukumar, wadda akwai bukatar samar da hukunci mai tsauri, kamar zaman gidan gyaran hali ga wadanda suka aikata laifukan da suka shafi rashin samar da ingantattun kayayyaki a kasar.
Salim wanda mataimakiyar darakta a hukumar, Mariam Samson ta wakilta, ta bayyana cewa idan aka yi wa dokar kwaskwarima za ta tabbatar da cewa masu sana’a da masu shigo da kayayyaki marasa inganci, baya ga yanke musu tara mai yawa, su ma za su fuskanci hukuncin dauri a gidan gyaran hali bisa girman laifin da suka aikata.