Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya mayar wa iyalan tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha filayen su guda 2 da tsohon gwamna Nasir El Rufai ya kwace a lokacin mulkinsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar lauyan iyalan tsohon marigayin shugaban kasar Reuben Atabo ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Sanarwar gwamnatin jihar Kaduna da Babban Daraktar ma’aikatar kula da filaye Mustapha Haruna ya gabatar tace, Gwamna Uba Sani ya rubutawa iyalan Janar Abacha wasika wanda aka sanya sunan Mohammed Sani Abacha, yana mai bayyana mayar musu da filayen da kuma gabatar musu da bukatar cewar su je su biya harajin da aka saba karba a hannun su na mallakar filayen.
- Hukumar Rawa Ta Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kirkirarriyar Fasahar Zamanin Kallon Al’adu
- Babu Sansanin Sojin Faransa a Maiduguri — Sojoji
An ce A shekarar 2022 ne dai tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufai ya gabatar da sanarwa a jarida ranar 28 ga watan Afrilu inda aka bayyana kwace filayen tare da soke takardun wadanda aka mallakawa a farko.