• Home  
  • Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri
- Babban Labari

Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri

A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al’ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani. Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya […]

A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al’ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani.

Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kafar Television ta RTN, inda ya ƙara da kira ga yan Nijar da su fahimci cewa jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a kowane ƙauye ba, duba da cewa Nijar na da kusan ƙauyuka 32,000.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan ta’adda musamman a kan sojojin ƙsar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai