Gwamnatin Kano ta amince da kashe sama da Naira biliyan 3 domin biyan kudin wasu ayyuka a faɗin jihar.
Kwamishinan yada Labarai na Jiha, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, inda ya yi nuni da cewa, sam hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar bai karya musu guiwa ba.
Kwamishinan ya bayyana hukuncin kotun a matsayin rashin adalci, inda ya ƙara da cewar, gwamnatinsu ta kudiri aniyar ci gaba da gudanar da manyan ayyukan da ta tsara a jihar nan.
A cewarsa, Wasu daga cikin manyan ayyuka da za a ci gaba da yi, akwai shirin aurar da Mata zaurawa sama da 1000 da shirin bayar da tallafin karatu na daliban jami’ar Bayero ta Kano na sama da Naira miliyan 712 da kuma biyan kudin jarrabawar kammala sakandire (SSCE) na sama da Naira miliyan 524.
Ya ce, za kuma a biya bashin wasu kudaden kwangila har Naira Miliyan 747.800 da ba a biya ba na kwangilar shekarar 2011 zuwa 2015.